2 Disamba 2015 - 05:06
An  sace 'yan mata a Borno

Gwamnatin jihar Borno ta nada wani kwamiti domin binciko rahotannin sace wasu 'yan mata a garin Bam-Buratai da ke karamar hukumar Biu ta jahar Borno.

Rahotanni sun ce a na kyautata zaton cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne su ka kara yin awon gaba da 'yan matan.

Kakakin gwamatin jihar Borno Isa Gusau ya shaidawa manema labarai  cewa matakin ya biyo bayan labaran da kafofin watsa labarai suka yadda a baya bayannan a kan cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun sake sace wasu 'yan mata a garin Bam-Buratai.

An dorawa kwamitin alhakin gano abin da ya faru a garin Bam- Buratai da kuma 'yan matan da ake zargin an sace.288